Hukumar ilmi, kimiyya da al'adu ta MDD wato UNESCO, mai helkwata a birnin Paris na kasar Faransa ta sanar jiya cewa, za a bai wa firaministan kasar Habasha Abiy Ahmed Ali lambar yabo ta zaman lafiya mai lakabin Felix Houphouet-Boigny na shekarar 2019, domin yaba wa gudummawarsa wajen tabbatar da zaman lafiya a shiyyar kasarsa.
Kwamitin ba da lambar yabo ya amince da gyare-gyaren da Abiy Ahmed Ali ya yi, domin inganta dimokuradiyya da hadin kan al'umma, musamman ma babbar gudummawarsa wajen kara azama kan cimma yarjejeniyar zaman lafiya a tsakanin kasarsa da kasar Eritrea.
Kwamitin ya yi fatan cewa, lambar yabon za ta karfafa gwiwar Abiy Ahmed Ali, ya ci gaba da himmantuwa wajen wanzar da zaman lafiya a shiyya-shiyya da ma duk nahiyar Afirka baki daya. (Tasallah Yuan)