Gebremariam wanda ya bayyana hakan yayin zantawarsa da kamfabnin dillancin labarai na Xinhua, ya ce kamfanin ET ya kuma kafa wani kwamitin hadin gwiwa da takwaransa na kasar Sin don duba irin ci gaban da aka samu game da sayen jiragen na C919.
Jami'in ya kuma bayyana cewa, kamfanin jiragen saman na ET yana aiki da gwamnatin kasar Sin , don mayar da Addis ababa, babban birnin kasar ta Habasha, a matsayin cibiyar fasahar kere-keren jiragen sama na kasar Sin a Afirka da kuma tsakanin Sin da Afirka a wannan fannin.
Ya kara da cewa, birnin Addis Ababa ba kawai zai zama wurin yada zangon jirage da kayayyaki ba, amma har ma zai zama cibiyar raya fasahar kere-keren jiragen saman kasar Sin a Afirka.
Kamfanin COMAC dai shi ne, babban kamfanin kera jiragen saman fasinja na kasar Sin.(Ibrahim)