Wata sanarwa da ofishin Firaministan kasar Abiy Ahmed ya fitar ce ta bayyana haka a jiya.
Sanarwar ta ruwaito Abiy Ahmed na cewa, layin dogon da ya hada Addis Ababa da Djibouti sakamako ne na farko-farko da shawarar Ziri Daya da Hanya Daya da Habasha ke ciki, ta haifar.
Ofishin ya bayyana ziyarar Firaminista Abiy Ahmed a kasar Sin, wanda wani bangaren ne na shawarar Ziri Daya da Hanya Daya, a matsayin mai muhimmanci, yana mai cewa, tuni ziyarar ta haifar da kyawawan sakamako ga kasar dake gabashin Afrika. (Fa'iza Msutapha)