Kasar Sin ce dai ta uku a yawan 'yan yawon shakatawa dake zuwa kasar Habasha, inda take bin bayan Amurka da Birtaniya. A bara yawan Sinawa da suka kai ziyara kasar ya karu da kaso 11.7 bisa dari, idan an kwatanta da Sinawa da suka shiga kasar a shekarar 2017, wadanda yawan su bai wuce 45,307 ba.
Darakta a ma'aikatar al'adu da yawon shakatawa, zamantakewar al'umma da huldar kasa da kasa Mr. Gezahegn Abate, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, samar da karin nau'oin abinci masu ban sha'awa, da wuraren saurar baki, za su taimaka wajen jawo karin Sinawa dake da sha'awar zuwa yawon bude ido kasar.
Mr. Abate ya ce ma'aikatar na fatan Sinawa masu zuba jari za su kara yawan kudin da suke shigarwa a sashen harkokin shakatawar kasar, ta yadda Sinawa za su kara nuna sha'awar su ta shiga kasar. (Saminu Alhassan)