in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An tallata bikin baje-kolin kayayyakin da ake shiga da fitar da su na kasar Sin a Habasha
2019-03-21 11:16:26 cri
An tallata bikin baje-kolin kayayyakin da ake shiga da fitar da su a kasar Sin,wanda aka fi sani da suna Canton Fair a turance,jiya Laraba a birnin Addis Ababa na kasar Habasha.

Shugaban sashin kula da mu'amala da masu sayayya na cibiyar gudanar da kasuwanci da kasashen waje ta kasar Sin Zhuang Hong ya bayyana cewa, ana kara kyautata bikin baje-koli na Canton Fair a 'yan shekarun nan, har ma ya samarwa baki 'yan kasuwa wani dandali na sayen kayayyaki kirar kasar Sin, da baiwa kamfanonin kasashen waje damammakin shiga kasuwannin kasar Sin da fadada harkokin kasuwanci a fadin duniya.

Babban jami'in kula da harkokin kasuwanci a ofishin jakadancin Sin dake Habasha, Liu Yu ya bayyana cewa, bikin Canton Fair ya zama muhimmiyar hanyar inganta cinikayya da kasuwanci tsakanin Sin da sauran kasashen duniya, kuma ana fatan Sin da Habasha za su yi amfani da wannan kyakkyawar dama don fadada mu'amalarsu a fannin kasuwanci. Ya kara da cewa, kasar Sin ta rika samar da damammaki ga kasashen Afirka, musamman lalubo wasu hanyoyin inganta kasuwanci tsakanin bangarorin biyu. A bana ma kasar Sin za ta kira bikin baje-kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin karo na biyu, inda ake fatan kamfanoni gami da kungiyoyin 'yan kasuwan kasar Habasha za su yi amfani da wannan zarafi don tallata kyawawan kayayyakinsu da fadada kasuwanci da kasar Sin.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China