Shaihin malami, kuma masani a fannin tattalin arziki Costantinos Bt. Costantinos, shi ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua.
Mr. Costantinos, wanda ya taba kasancewa mashawarci ga kungiyar AU, da hukumar MDD mai lura da raya tattalin arzikin Afirka ko ECA, ya ce sama da ko wace kasa a nahiyar Afirka, Habasha ce kan gaba wajen cin gajiyar shawarar ziri daya da hanya daya, musamman idan aka yi duba da layin dogo na Addis Ababa zuwa kasar Djibouti da aka gina karkashin wannan shawara, da ma sauran manyan ayyukan raya kasa.
Masanin ya kuma bayyana cewa, dandalin da za a gudanar a birnin Beijing, zai zamo wata hanyar karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashe daban daban karkashin inuwar shawarar ta ziri daya da hanya daya.
Kalaman na Costantinos na zuwa ne, a gabar da gwamnatin kasar Habasha ke cewa, ta shirya halartar dandalin, da wata muhimmiyar tawaga wadda za ta kunshi firaministan kasar Abiy Ahmed, da sauran manyan wakilan gwamnati.(Saminu Alhassan)