in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanin Ethiopian Airlines ya mai da martani game da zargin rashin horo da ake matukin jirginsa da ya yi hatsari
2019-03-22 10:52:17 cri
Kamfanin jiragen sama na Ethiopian Airlines, ya yi watsi da wani rahoto dake cewa ba a horar da matukin jirgin Boeing 737 Max 8, da ya yi hatsari a baya-baya nan ba, yana mai bayyana batun a matsayin karya, wanda kuma bai dace ba.

Jirgin MAX 8 mallakar kamfanin ya fadi ne jim kadan bayan tashinsa daga Addis Ababa babban birnin Habasha a ranar 10 ga watan Maris, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane 157 da yake dauke da su.

Yayin da ake tsaka da gudanar da bincike, wasu rahotanin dake fitowa a baya-bayan nan, na nuni da cewa, duk da kamfanin na Ethiopian Airlines na daga cikin wadanda suka fara sanya manhajar horo a sabon jirgin na Max 8, babban matukin jirgin ET-302 da ya fadi bai karbi horon ba.

Sai dai, kamfanin ya jadadda cewa, irin wadannan rahotannin ba su da gaskiya, kuma ba su dace ba, sannan za su iya yin tasiri kan binciken da ake gudanarwa.

Kamfanin ya ce dukkan matukansa sun kammala karbar horon da kamfanin kera jiragen sama na Boeing da hukumar kula da sufurin jiragen sama ta Amurka (FAA) suka bada shawarar yi, daga na jirgin B-737 NG zuwa na B-737 MAX, kafin ma a kaddamar da jirgin B-737 8 MAX, kafin daga bisani su fara tuka jirgin na B-737-8 Max.

Kamfanin Ethiopian Airlines ya kara da cewa, an kuma yi wa matukan bayani sosai, game da matakan da za su bi a lokacin bukata ta gaggawa da hukumar FAA ta gabatar, biyo bayan hatsarin da makamancin jirgin na kamfanin jiragen sama na Lion Air ya yi.

Haka zalika, an sanya matakan cikin daftarorin bayanan jirgin da na amfani da shi da kuma yadda za a tafiyar da shi. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China