Ministan man fetur na kasar Sudan ta Kudu Ezekiel Lol Gatkuoth ya bayyana wa wakilin kamfanin dillancin labaru na Xinhua cewa, kasarsa ta gode wa kokarin da kamfanin man fetur da iskar gas na kasar Sin wato CNPC ya yi wajen sake dawo da aikin hakar danyen mai a filayen hakar man fetur na kasar, lamarin da zai taimakawa kasarta Sudan ta Kudu ta kama hanyar farfado da tattalin arzikinta cikin sauri. Ministan ya kuma nuna cewa, sakamakon dawo da aikin hakar man fetur a filayen hakar man El Toor da Manga da za a yi a karshen watan Mayun bana daya bayan daya, ya sa ana sa ran ganin yawan danyen man fetur da kasar Sudan ta Kudu take hakowa a kowace rana zai karu da ganga dubu 70 baki daya. (Tasallah Yuan)