in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ababen fashewa miliyan1 aka lalata a Sudan ta Kudu tun daga shekarar 2004
2019-01-31 14:01:04 cri

Hukumar MDD dake rage barazanar ababen fashewa UNMAS, ta ce ta lalata nakiyoyi da ababen fashewa miliyan1, tun bayan da ta fara aiki a kasar Sudan ta kudu, shekaru 14 da suka gabata.

Da yake jawabi yayin bikin kawar da ababen fashewa 1,000,000 a jiya Laraba, Richard Boulter, manajan shirin UNMAS a Sudan ta kudu, ya ce an samo abubuwan da aka lalata ne a yankin da ya kai fadin murabba'in mita biliyan 1, wanda a baya haduran ababen fashewa suka gurbata.

Richard Boulter ya kara da cewa MDD na kokarin aiki kan wani yankin da ya kai murabba'in kilomita 39 wanda ya gurbace da ababen fashewa, cikin shekaru 5 masu zuwa.

A cewar UNMAS, rikicin da aka shafe gomman shekaru ana yi a Sudan ta Kudu, ya lalata yankin da ya kai fadin murabba'in mita kusan miliyan 90 da ababen fashewa. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China