in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan ta Kudu na neman zama mamban WTO domin gaggauta ci gabanta
2019-04-17 10:11:22 cri

Kasar Sudan ta Kudu ta ce, kara shiga harkokin cinikayya a yankinta da ma duniya, zai taimaka wajen samar da ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al'ummar kasa da take bukata, wanda kuma zai inganta tsaro a kasar, bayan shafe shekaru 5 ana rikici.

Mataimakin Sakataren ma'aikatar kula da cinikayya da harkokin kungiyar raya yankin gabashin Afrika (EAC), Mou Mou Athian, ya shaida wa wasu 'yan kasuwa a birnin Juba cewa, bayan shiga kungiyar EAC, yanzu kasar na kokarin zama mamban kungiyar kula da cinikayya ta duniya WTO, wanda zai samar da jari da kasuwa ga abubuwan da ake sarrafawa a kasar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China