in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mata a Sudan ta Kudu sun yi kira da daidaiton jinsi domin rage yawan cin zarafinsu
2019-03-08 10:20:07 cri

Mata a kasar Sudan ta Kudu sun yi kira da tabbatar da daidaiton jinsi cikin manufofin zaman lafiya domin gaggauta wanzar da tsaro da kuma taimakawa wajen rage yawan cin zarafinsu.

Shugabar rundunar 'yan sanda masu wanzar da zaman lafiya na MDD wato UNMISS, Unaisi Lutu Vuniwaqa, ta ce ya kamata karin mata su jagoranci wanzar da dawwamamen zaman lafiya, tun da suna da kyakkyawan tasiri wajen tabbatar da zaman lafiya a kasar, biyo bayan yarjejeniyar farfado da zaman lafiya da aka rattaba hannu cikin watan Satumban bara a kasar Habasha.

Unaisi Lutu Vuniwaqa, ta bayyana jiya a Juba yayin wani taron tattaunawa gabanin ranar mata ta duniya da ake yi a yau Jumma'a cewa, yayin da ake tunkarar karshen lokacin mika ragamar tsaron kasar, akwai bukatar dukkan bangarori a kasar, su kara zage damtse wajen nada kwararru mata da suka shirya yin aiki kafada da kafada da maza domin samun karin moriya.

Jami'ar ta ce ya kamata gwamnatin ta tabbatar da daidaitoin jinsi a dukkanin ma'aikatu a ko wane mataki. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China