in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana fatan kafuwar gwamnatin hadaka ta Sudan ta kudu a watan Mayu duk da irin kalubalen da ake fuskanta
2019-03-21 10:38:14 cri
Mahukunta a Sudan ta kudu, na cewa za a kafa gwamnatin hadin kan kasa cikin watan Mayu mai zuwa, duk kuwa da shakku da sassan 'yan adawa ke nunawa game da yiwuwar hakan.

Da yake tsokaci game da wannan batu, ministan watsa labaran kasar Michael Makuei Lueth, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, za a aiwatar da wannan manufa, duk da jinkirin amincewar sassan masu ruwa da tsaki, game da adadin sojojin da bangarorin za su shigar cikin rundunar gwamnatin hadakar, da batun hade rundunar sojojin kasar, da batutuwa masu nasaba da kan iyakoki.

Michael Makuei Lueth, ya ce ko da ba a kai ga hade rundunar sojojin kasar ba nan da watan na Mayu, za a zartas da kudurin kafa gwamnatin hadin kan kasa kamar yadda aka tsara.

Ministan wanda ya bayyana hakan a birnin Juba, ya ce rashin cimma matsaya da 'yan adawa game da takamaiman adadin dakarun su da za a shigar cikin rundunar sojin kasar, ya kawo tsaiko wajen kafa sansanonin sojin kasar a sassa daban daban.

Gabanin hakan, mataimakin shugaban ofishin watsa labarai na babbar kungiyar 'yan adawar kasar ko SPLM-IO a takaice, Mr. Manawa Peter Gatkuoth, ya ce zai yi wuya a kai ga kafa gwamnatin hadin kan kasa nan da watan Mayu, wato lokacin da wa'adin gwamnatin rikon kwaryar zai kare, duba da yadda aka gaza kafa sansanonin dakarun sojin kasar, da ba da horo, tare da hade sassan rundunar sojojin wuri guda. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China