in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta bada gudunmuwar shinkafa ton 9,600 ga Sudan ta Kudu
2019-02-22 10:17:40 cri
Gwamnatin kasar Sin, ta bada gudunmuwar kimanin ton 9,600 na shinkafa ga Sudan ta Kudu, domin taimakawa fararen hula dake fuskantar barazanar yunwa a kasar mafi kankantar shekaru a duniya, wadda kuma ake kokarin sake ginata bayan shafe shekaru kusan 5 ana fama da yakin basasa.

Shugaban hukumar bada agaji da sake tsugunar da mutane na kasar, Manasseh Lomole, ya ce tuni kashin farko na shinkafar ya isa Juba babban birnin kasar, sannan kuma ragowar za su isa daga baya.

Za a mika gudunmuwar abincin ne ga wadanda suka koma bayan gudun hijara da wadanda suka rasa matsugunansu da kuma wadanda suka rayu bayan aukuwar ambaliya da fari. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China