in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan ta kudu ta sha alwashin kawo karshen shigar da kananan yara ayyukan soji
2019-02-20 10:13:52 cri
Jiya Talata Sudan ta kudu ta lashi takobin kawo karshen yin amfani da kananan yara wajen ba su makamai don shigar da su yaki a yayin da kasar ke ci gaba da daukar matakan kawo karshen yakin basasar kasar da ya shafe sama da shekaru biyar.

Kuol Manyang Juuk, ministan tsaro da kula da harkokin sojojin da suka yi ritaya na kasar, ya ce sashen baiwa yara kariya na hukumar sojoji ta kasar yana ci gaba da aiki babu kakkautawa tare da kwamandojin sojojin kasar domin tsame kananan yara daga ayyukan yaki.

Ya kara da cewa, gwamnatin kasar ta bayar da umarni ga dukkan manyan janar janar na sojojin kasar da su bada hadin kai ga hukumomin MDD da abin ya shafa domin tabbatar da ganin an dakile shigar da kananan yara ayyukan soji, yana mai cewa, dakarun wanzar da tsaron jama'ar kasar Sudan ta kudu (SSPDF) ta horar da wasu jami'anta masu baiwa yara kariya sama da 100 a yunkurin da take na inganta aikin soji.

"Wannan daya ne daga cikin matakan da ake dauka domin tsabtace hanyoyin ingancin aikin soji. Ba mu da wani zabin da ya wuce samar da ingantacciyar rundunar sojoji, rundunar sojin da za ta kare hakkin dan adam da dukiyoyin al'ummar kasa," Juuk ya bayyana hakan a Juba.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China