Geng Shuang, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana yau Talata a nan Beijing cewa, kasar Sin na tafiyar da harkokinta bisa doka. Gwamnatin Sin ta bai wa jama'arta 'yancin bin addini. Al'ummar kabilu daban daban na kasar Sin, suna yin addinansu cikin 'yanci. Sa'an nan kuma kasar Sin ta hana a aikata laifi da sunan addini. Kasar Sin ta kalubalanci kasar Amurka da ta daina tsoma baki cikin harkokin cikin gidanta da sunan addini.
Kwanan baya, kwamitin kula da 'yancin yin addini na Amurka ya kaddamar da rahoton shekara-shekara na shekarar 2019, inda ya soki yadda ake tafiyar da harkokin addini a kasar Sin. (Tasallah Yuan)