Wani sabon rahoto game da kuri'ar jin ra'ayin jama'a da aka gudanar a kasar Amurka, ya nuna yadda jama'a a duniya suka nuna amincewa da shugabancin kasar Sin fiye da na Amurka a shekarar 2018 da ta gabata, inda kaso 34 cikin 100 suka nuna amincersu da shugabancin kasar Sin, alkaluma mafi yawa a cikin kusan shekaru 10.
Rahoton, mai suna matsayin shugabannin duniya na shekatar 2019, wanda ya nuna yadda jama'a a kasashe 133 suke kallon matsayin shugabancin kasashen Amurka, Sin da Jamus da Rasha, inda kasar Sin ta samu kaso 34 cikin 100 na wadanda suka amince da shugabancin kasar, maki mafi yawa da wata kasa ta samu tun shekarar 2009, yayin da matsakaicin makin da Amurka ta samu ya yi kasa zuwa kaso 31 cikin 100.
Kasar Sin ta samu maki mafi yawa ne a Afirka, inda matsakaicin makin amincewar da ta samu ya kai kaso 53 cikin 100. Sai dai tsakanin shekarar 2017 da 2018, shugabancin kasar Sin ya samu karuwar kaso 10 ko fiye a kasashe 14 na amincewa da shugabancin kasar.(Ibrahim)