Kakakin ya bayyana haka ne, a yayin taron manema labaru da aka shirya a yau Alhamis, inda ya kara da cewa, tawagar wakilan cinikayyar kasar Amurka za su iso nan birnin Beijing a wannan rana, don halartar shawarwarin tattalin arziki da cinikayya bisa babban matsayi a tsakanin kasashen biyu a zagaye na 8, wanda za a gudanar a gobe Jumma'a, kana a mako mai zuwa, mataimakin firaministan kasar Sin, kuma mai jagoran shawarwarin na bangaren Sin Liu He, zai kai ziyara Washington, don yin shawarwari a zangaye na 9 tare da bangaren Amurka.
Baya ga haka, kakakin ya kara bayyana cewa, ko da yaushe kasar Sin na cike da imanin cewa, hadin kan juna shi ne zabi mafi dacewa ga kasashen Sin da Amurka, saboda baya ga amfanawa jama'ar kasashen biyu, zai kuma amfanawa duniya bakin daya. (Bilkisu)