in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kammala tattaunawar manyan jami'an Sin da Amurka kan tattalin arziki da ciniki karo na 9
2019-04-07 16:11:14 cri

Daga ranar 3 zuwa 5 ga wata, Liu He, mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kana mataimakin firaministan kasar, kuma mai jagoran tawagar Sin a tattaunawa tsakanin kasashen Sin da Amurka kan tattalin arziki daga sassa daban daban, da Robert Lighthizer, wakilin kasar Amurka kan harkokin cinikayya da kuma Steven Mnuchin, ministan kudi na Amurka sun shugabanci tattaunawar manyan jami'an Sin da Amurka kan tattalin arziki da ciniki karo na 9 cikin hadin gwiwa a birnin Washington na Amurka, inda bangarorin 2 suka samu sabon ci gaba kan abubuwan da za a tanada cikin yarjejeniyoyi masu nasaba da musayar fasaha, kiyaye ikon mallakar fasaha, matakan da za a dauka kan harkokin cinikin da ba na buga haraji ba, aikin ba da hidima, aikin gona, daidaiton ciniki, tsarin aiwatarwa da dai sauransu. Har ila yau bangarorin 2 sun tsaida kudurin ci gaba da tattaunawa ta dukkan hanyoyin da suka dace kan batutuwan da suka rage. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China