Kakakin ma'aikatar harkokin kasuwanci ta kasar Sin Gao Feng ya bayyana a jiya Alhamis a birnin Beijing, cewar bayan da aka kawo karshen shawarari karo na tara a tsakanin Sin da Amurka kan batun tattalin arziki da cinikayya, shugabannin tawagogin bangarorin biyu sun tattauna ta wayar tarho kan batutuwan da ba a warware ba tukuna.
Daga ranar 3 zuwa 5 ga wata, mataimakin firaministan kasar Sin Liu He da wakilin Amurka kan batun cinikayya Robert Lighthizer da sakataren kudi ta Amurka Steven Mnuchin su ne suka jagoranci shawarwari karo na tara a birnin Washington, hedkwatar mulkin Amurka.
Mr. Gao Feng ya kuma bayyana cewa, bangarorin biyu sun tattauna kan batutuwan kare 'yancin mallakar fasaha, musayar fasahohi, matakan da za a dauka wanda bai shafi haraji ba, aikin ba da hidima, ayyukan noma, samun daidaiton ciniki, da bullo da wani tsari, wadanda aka samu sabon ci gaba a kai. Bangarorin biyu za kuma su ci gaba da yin shawarwari kan batutuwan da suka rage, dangane da matsayar da shugabannin kasashen biyu suka cimma a baya.(Kande Gao)