in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi ya ce an cimma manyan nasarori game da shawarwari tsakanin Sin da Amurka
2019-04-05 15:52:52 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ce an cimma sabbabi kuma manyan nasarori, a tattaunawar da wakilan Sin da na Amurka ke yi, don gane da batutuwan da suka shafi tattalin arziki da cinikayya cikin sama da kwanaki 30 da suka gabata.

Cikin wani sako na shugaba Xi da mataimakin firaministan Sin Liu He ya gabatarwa shugaba Donald Trump na Amurka a fadar White House dake Amurka a ranar Alhamis, shugaban na Sin ya ja hankalin wakilan sassan biyu da su kara azama, wajen aiki tukuru, tare da martaba juna, da daukar juna matsayi guda, da cimma moriya tare. Kaza lika su kuma tabbatar da daukar matakan warware sabanin da ke tsakanin kasashen biyu, kana su kammala shawarwari game da batutuwan da ake da sabani a kan lokaci.

Yayin ganawar sa da shugaba Trump, Mr. Liu ya ce wakilan Sin da na Amurka, sun zanta da juna a kai a kai, sun kuma cimma matsaya game da wasu muhimman batutuwa dake shafar yarjejeniyar tattalin arziki da cinikayyar sassan biyu.

A nasa bangaren kuwa, shugaba Trump na Amurka, ya ce ya lura da manyan nasarori da aka samu a yayin tattaunawar sassan biyu, yana mai fatan wakilan kasashen za su kara azama, wajen ganin sun warware sauran batutuwan da ake da sabani a kan su, ta yadda za a kai ga cimma cikakkiyar yarjejeniya mai cike da tarihi nan ba da jimawa ba.

Ya ce hakan zai yi matukar amfanar Sin da Amurka, da ma sauran sassan duniya baki daya. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China