in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
#BRF2019# Xi Jinping: Kafa dangantakar abokantaka ta mu'ammala da juna a duniya wani muhimmin abu ne na raya BRI
2019-04-26 10:30:19 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana a yau Juma'a cewa, abu mai muhimmanci wajen raya shawarar "Ziri daya da hanya daya" wato BRI, shi ne yin mu'ammala tsakanin kasa da kasa, ya kamata a kafa dangantakar abokantaka ta mu'amala a duniya baki daya, don cimma burin samun ci gaba da wadata tare. Kasar Sin za ta ci gaba da hada kai da bangarori daban daban don kafa wani tsarin mu'ammala dake dogaro kan hanyar dogo, tashar jiragen ruwa, da kuma sarafar bututun mai da dai sauransu. Kasar Sin za ta ci gaba da taka rawa a fannin asusun zuba jari na musamman iri daban daban, da bunkasa takardu masu daraja game da batun hanyar siliki, da nuna goyon baya ga cibiyar hadin kai ta habaka da harkokin kudi ta bangarori da dama wajen gudanar da aiki yadda ya kamata, tana kuma maraba da hukumomin kudi na bangarori da kasashe daban daban su shiga ayyukan na zuba jari ko tattara kudi game shawarar "Ziri daya da hanya daya", kana da kara wa kasuwar bangare na uku kwarin gwiwa wajen gudanar da hadin kai. (Bilkisu)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China