in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yankin cinikayya cikin 'yanci na Lekki ya karyata zargin da kasashen yamma suka yi
2019-04-25 15:52:16 cri
A yau Alhamis ne, aka shirya dandalin tattaunawa kan hadin kan tattalin arziki da cinikayya dake ketare na taron kolin dandalin tattaunawar kasa da kasa game da shawarar "Ziri daya da hanya daya" karo na biyu a nan birnin Beijing, inda mataimakin manajan kamfanin CCECC, kuma babban manajan kamfanin zuba jari na Lekki na Sin da Afirka Chi Changgui ya ce, ya zuwa karshen watan Maris na bana, a matsayinsa na daya daga cikin yankunan hadin kan tattalin arziki da cinikayyar kasar Sin dake ketare a karon farko, yankin cinikayya cikin 'yanci na Lekki da Sin da Najeriya suka kafa tare, ya jawo kamfanonin Sin da kasashen ketare guda 138, yawan jarin da kamfanonin suka zuba ya kai dalar Amurka miliyan 191, yawan harajin da suka biya gwamnatin Najeriya ya kai Naira biliyan 12.4, wanda kuma ya samar da guraban ayyukan yi sama da 1500. A sa'i daya kuma, yankin yana himmatuwa wajen inganta rayuwar mazauna wurin, inda ya kuma kafa wani asusun bunkasa al'ummomi, don tallafawa al'ummomin dake dab da shi a fannonin gyara hanyoyin mota, kyautata muhallin amfani da ruwa, ba da tallafin kudi ga daliban Najeriya wajen yin karatu a kasar Sin, da kuma horas da ma'aikatan kamfanonin yankin na bangaren Najeriya da wasu jami'an gwamnati a kasar Sin da dai sauransu. Wadannan ayyukan da yankin cinikayyar cikin 'yanci ya gudanar na goyon bayan ci gaban tattalin arziki da zaman al'ummar wurin, sun mayar da martani kan zargin da wasu kasashen yamma suke yi wai "Sin tana yada wani sabon salo na mulkin mallaka a Afirka". (Bilkisu)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China