in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron kolin BRF karo na biyu
2019-04-26 10:14:13 cri

A yau Jumma'a a nan birnin Beijing, an bude taron kolin dandalin tattaunawar hadin kan kasa da kasa kan shawarar ziri daya da hanya daya a karo na biyu, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da jawabi.

Ziri daya da hanya daya shawara ce da shugaba Xi Jinping ya gabatar dangane da hadin kan tattalin arzikin kasa da kasa. A cikin shekaru shida da suka wuce, jimillar cinikin da aka yi tsakanin Sin da kasashen da suka karbi shawarar ziri daya da hanya daya ya zarce dalar Amurka triliyan 6, a yayin da jarin da ta zuba wa kasashen ya kai dalar Amurka biliyan 80. Har wa yau, an kuma samar da guraben ayyukan yi kimanin dubu 300 ga kasashen bisa ga shirye-shiryen hadin gwiwarsu.

Za a shafe tsawon kwanaki uku ana taron, kuma jigon taron shi ne "raya ziri daya da hanya daya, don samar da kyakkyawar makoma". Baki kusan dubu 5 za su halarci taron, ciki har da shugabanni da kusoshin gwamnati da suka zo daga kasashe 37 da babban sakataren MDD da babbar darektar asusun ba da lamuni na duniya da sauransu. (Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China