Wu ya bayyana hakan ne yayin taron manyan jami'an babban zauren MDD, na murna da yayata ranar alakar kasa da kasa da matakan diflomasiyya don samar da zaman lafiya da aka yi a jiya.
Ya ce, shawarar ziri daya da hanya daya, ta bunkasa tsarin kasancewar bangarori daban-daban a sabon zamanin da ake ciki.
Kalaman jami'in na kasar Sin dai, na zuwa ne a jejiberin taron kolin dandalin hadin gwiwar kasa da kasa game da shawarar da zai gudana daga yau zuwa 27 ga wata a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.
Ya ce, MDD ita ce alamar kawancen kasa da kasa, kuma kasar Sin na fatan MDD za ta jagoranci wanzuwar zaman lafiya a duniya, da karfafa bunkasuwa ta bai daya da zurfafa hadin-gwiwar kasa da kasa.(Ibrahim)