in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
#BRF2019#Xi Jinping: rashin daidaito a fannin ci gaba ita ce babbar matsalar da muke fuskanta a duniya
2019-04-26 10:26:30 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana a yau Jumma'a a nan birnin Beijing cewa, rashin daidaito a fannin ci gaba ita ce babbar matsalar da muke fuskanta a duniya. A yayin da sassa daban daban ke kokarin raya ziri daya da hanya daya, kamata ya yi a cusa ra'ayin nan na samun dauwamammen ci gaba cikin ayyukan da ake gudanarwa, haka kuma ya kamata kasa da kasa su dukufa wajen yin hadin gwiwa, don samar da karin damammaki ga kasashe masu tasowa, ta yadda za a fid da su daga kangin talauci da kuma tabbatar sun samu dauwamammen ci gaba. Baya ga haka, ya kamata a inganta hadin gwiwa da MDD ta fannin ci gaba, don kokarin cike gibin da ake fuskanta a wannan fannin.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China