in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya gana da takwaransa na Kenya
2019-04-25 15:19:28 cri

Yau Alhamis, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na kasar Kenya Uhuru Kenyatta a nan birnin Beijing.

A yayin ganawar, shugaba Xi ya nuna cewa, kasarsa ta nuna yabo ga shugaba Uhuru Kenyatta da ya sha karyata zargin da aka yi game da hadin kai a tsakanin Sin da Kenya da Sin da Afirka. A cewarsa, Kenya kasa ce da tuni ta sanya hannu kan takardar fahimtar juna game da raya shawarar "Ziri daya da hanya daya" tare da kasar Sin. Kasar Sin na son amfani da damar raya shawarar "Ziri daya da hanya daya" da tabbatar da nasarorin da aka cimma a yayin taron kolin Beijing na dandalin tattaunawar hadin kai a tsakanin Sin da Afirka, kana da hada kai tare da Kenya don kiyaye yanayi mai kyau da ake ciki na hadin kai a tsakanin Sin da Kenya da Sin da Afirka.

A nasa bangaren, shugaba Uhuru Kenyatta ya bayyana cewa, shawarar "Ziri daya da hanya daya" ta inganta mu'amalar cinikayya da kafa ingantacciyar huldar abokantaka a tsakanin kasashe daban daban, wadda ta samu amincewar kasashen duniya, ta kuma inganta yunkurin cudanya da masana'antun kasashen Afirka. Kasar Kenya tana son karfafa hadin kai tare da Sin a fannin muhimman kayayyakin more rayuwa da dai sauransu, don yada shawarar "Ziri daya da hanya daya" zuwa yankunan tsakiya da yammacin nahiyar Afirka. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China