in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaddamar da taruka 12 na dandalin hadin gwiwa bisa shawarar ziri daya da hanya daya karo na 2
2019-04-25 20:33:45 cri

Yau Alhamis an kaddamar da taron dandalin koli kan hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa, bisa shawarar ziri daya da hanya daya karo na 2 a hukumance a nan birnin Beijing, inda aka shirya taruka guda 12 domin gudanar da cikakkiyar tattaunawa, kan batutuwan dake shafar cudanyar bangarori biyar, wato tsara manufa, da aikin gina kayayyakin more rayuwa, da cinikayya, da hada-hadar kudi, da kuma zumunci tsakanin al'ummu.

Sauran batutuwan sun kunshi yaki da cin hanci da rashawa, da raya fasahohin zamani, da kiyaye muhalli, da kirkire-kirkire, da kuma hadin gwiwar dake tsakanin yankuna, ta yadda za a cimma matsaya guda kan su.

Mataimakin darektan hukumar raya kasa da yin kwaskwarima ta kasar Sin Ning Jizhe ya bayyana cewa, yanzu haka an riga an sauya shawarar ziri daya da hanya daya daga tunani zuwa hakikanin aiki, ba ma kawai kasar Sin tana himmantu kan aikin gina kayayyakin more rayuwa bisa manyan tsare-tsaren da ta gabatar, wato kafa manyan yankunan hadin gwiwar tattalin arziki guda shida, tsakanin kasashen nahiyoyin Asiya da Turai, tare kuma da gina layin dogo, da hanyar mota, da hanyar ruwa, da hanyar jirga-jirgar jiragen sama, da fannin sadarwa tsakanin kasashen da abun ya shafa, haka kuma za ta kara dora muhimmanci kan cudanyar dake tsakaninta da sauran kasashen duniya, bisa tushen martaba manufofi da ka'idojin kasa da kasa.

Bisa ci gaban aikin aiwatar da shawarar ziri daya da hanya daya, ana gudanar da wasu manyan ayyuka lami lafiya, a don haka aikin tattara kudi da magance rikicin bashi ya kara jawo hankalin jama'a.

Yau a hukumance ma'aikatar kudin kasar Sin ta fitar da tsarin tantance bashi bisa shawarar ziri daya da hanya daya, domin samarwa bangarori daban daban da suka shiga shawarar hanyoyin tantance dabarun daidaita bashi, ta yadda za su sanya kokari tare da sauran kasashen duniya, domin samun kudin da suke bukata yayin da suke kokarin cimma burin karuwar tattalin arziki a kasashensu bisa shawarar ziri daya da hanya daya.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China