in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
WHO: barkwar cutar Ebola a Congo (Kinshasa) ba wani batun gaggawa ne da ya shafi lafiyar al'umma da ke jan hankalin duniya ba
2019-04-13 17:02:11 cri

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce, ko da yake mutanen da suka kamu da cutar Ebola ya dan karu a kasar Congo (Kinshasa) a makonni da dama da suka wuce, ya zuwa yanzu, barkewar annobar a kasar, ba wani batun lafiyar al'umma na gaggawa da ke jan hankalin duniya ba ne. Duk da haka an bukaci sassa daban daban su rubanya kokarinsu wajen yaki da annobar.

Babban sakataren WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya kira taron kwamitin kula da batutuwan gaggawa na WHO dangane da barkewar Ebola a Congo (Kinshasa) bisa abubuwan da aka tanada cikin "ka'idojin kiwon lafiya na duniya". Ko da yake kwamitin yana ganin cewa, ya zuwa yanzu, barkewar cutar a Congo (Kinshasa) ba wani batun ne na gaggawa ba, ya nuna damuwa kan karuwar masu kamuwa da ita a wasu wurare na kasar a kwanakin baya, saboda akwai yuwuwar ta yadu zuwa kasashe masu makwabtaka da kasar. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China