Sa'o'i kalilan bayan harin na ranar Asabar, Tedros Adhanom ya yi rangadin cibiyar birnin Butembo, wadda ita ma aka far mata a makon da ya gabata, inda ya godewa ma'aikatan cibiyar saboda jajircewarsu.
Darakta Janar din ya ce, yayin da ake ci gaba da makokin wadanda suka mutu a harin da aka kai a baya, a kokarinsu na kare hakkin lafiya, tuna jami'an lafiya da suka ji rauni da 'yan sandan da suka mutu a harin na taba masa zuciyarsa.
Ya kara da cewa, babu wani zabi, ban da ci gaba da yi wa jama'ar kasar hidima, wadanda ke cikin mutanen da suka fi rauni a duniya.
Har ila yau, jami'in ya ce WHO ta nema, kuma ta samu karin tallafi daga MDD da jami'an tsaro na yankin, domin kare cibiyoyin. (Fa'iza Mustapha)