in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Cutar Ebola ta hallaka sojoji 2 a jamhuriyar dimokaradiyyar Congo
2019-01-30 19:57:24 cri
Wata majiyar rundunar sojojin jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, ta ce dakarunta biyu sun rasu a gabashin kasar, sakamakon kamuwa da cutar Ebola mai saurin kisa.

Kakakin rundunar na yankin Beni dake lardin arewaci Kivu Mak Hazukay, ya ce akwai wasu karin sojojin 3 da ake lura da su, domin tabbatar da matsayin su game da cutar. Mr. Hazukay ya kara da cewa, ana daukar dukkanin matakan da suka wajaba, domin dakile yaduwar wannan cuta tsakanin sojojin kasar.

Tun sake bullar wannan annoba, jimillar alkaluman ta sun kai 736, ciki hadda mutum 682 da aka tabbatar sun harbu, da wasu 54 dake matsayin kila-wa-kala.

Ma'aikatar lafiyar kasar ta ce tuni cutar ta haddasa rasuwar mutane 459, da suka kunshi mutum 405 wadanda aka tabbatar cutar ce ta hallaka su, da wasu 54 da ba bu tabbas kan hakan, baya ga wasu 257 da suka warke bayan kamuwa da cutar. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China