Shugaban kasar Rwanda, kuma jagoran karba karba na kungiyar AU Paul Kagame ne ya jagoranci taron na birnin Addis Ababa fadar mulkin kasar Habasha. Kaza lika taron ya samu halartar firaministan Habasha Abiy Ahmed, da shugaban Afirka ta kudu Cyril Ramaphosa, da shugaba Yoweri Museveni na kasar Uganda.
Da yake tsokaci yayin bude taron, shugaba Kagame ya jinjinawa kokarin shugabannin kasashe mambobin kungiyar SADC, na zakulo hanyoyin warware sabanin da ya biyo bayan zaben Congo, yana mai nanata bukatar da ake da ita, ta hadin kan daukacin kasashen Afirka wajen shawo kan matsalolin nahiyar.
Shi kuwa shugaban hukumar zartaswar kungiyar AU Moussa Faki Mahamat, cewa ya yi da damu mataka, game da yanayin da ake ciki a janhuriyar dimokaradiyyar Congo, kuma taron na wannan karo, mataki ne na nuna goyon baya ga kasar. (Saminu Alhassan)