in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
WHO ta nemi taimakon kasa da kasa a yayin da aka samu bullar cutar Ebola kusan dubu 1 a DRC
2019-03-24 16:38:03 cri
Hukumar lafiya ta duniya (WHO), a ranar Asabar ta bukaci taimakon gaggawa na kasa da kasa domin tunkarar annobar cutar Ebola a jamhuriyar demokaradiyyar Kongo (DRC), inda ake tsammanin adadin wadanda suka kamu da cutar ya kai kusan mutane 1,000.

Tun bayan da aka ayyana barkewar cutar Ebola a DRC a watan Augastan shekarar 2018, adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar da wadanda ake hasashen sun kamu sun kai 993, inda aka samu mutuwar mutane 621.

Ko da yake, an yiwa mutane sama da 96,000 alluran rigakafi a kasar, kana tantancewar da aka yiwa mutane sama da miliyan 44 a kan iyakokin kasar ya taimaka matuka wajen takaita saurin bazuwar cutar ta Ebola, hadarin dake tattare da yaduwar cutar ga kasar dama shiyyar yana da girman gaske, musamman a yayin da ake samun karuwar tashe tashen hankula da rashin zaman lafiya a yankunan kasar.

A halin yanzu hukumar lafiya ta MDD tana da jami'ai sama da 700 a Kongo DRC, inda suke ta kokarin shawo kan matsalar a yankunan da lamarin ya shafa. Amma fargabar da suke da shi game da barkewar tashin hankali ya kara jefa fargaba wajen yaki da cutar ta Ebola, in ji Dr. Tedros.

Babban jami'in na hukumar WHO ya ce, duk da irin karuwar hare haren kungiyoyin masu dauke da makamai, WHO zata cigaba da tsayawa tsayin daka wajen aiki tukuru da al'ummomin yankunan da matsalar ta shafa don kawo karshen annobar tare da hadin gwiwar ma'aikatar lafiyar kasar da sauran hukumomin bada agaji na ciki da wajen kasar.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China