in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jakadan Sin ya bukaci taimakon kasa da kasa don tabbatar da zaman lafiyar Kongo
2019-01-12 15:06:41 cri
A jiya Juma'a jakadan kasar Sin ya bukaci al'ummar kasashen duniya da su ci gaba da taimakawa gwamnatin jamhuriyar demokaradiyyar Kongo DRC (DRC), wajen tabbatar da dorewar zaman lafiya da kwanciyar hankali a daidai lokacin da kasar ke cikin muhimmin lokaci bayan da aka kammala babban zaben kasar.

Ya kamata kasa da kasa su ci gaba da nuna girmamawa ga ikon mulkin kasa, da 'yancin kasa, da kuma mutunta 'yancin da kasar Kongo ke da shi na iko da yankunanta da kuma hakkin da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar ke da shi, Ma Zhaoxu, zaunannen wakilin kasar Sin a MDD, shi ne ya bayyana hakan ga kwamitin sulhun MDD.

"Muna daukar zabe a matsayin wani al'amari ne da ya shafi harkokin cikin gidan kasa. Mun yi amanna cewa, al'ummar kasar Kongo suna da dama da kuma hikimar da za su iya warware batutuwan da suka shafe su da kansu. Muna fata dukkan bangarorin da abin ya shafa a Kongo za su kwantar da hankalinsu, su kai zuciya nesa, kana su kawar da duk wasu banbance banbance dake tsakaninsu ta hanyar tattaunawar sulhu da juna domin lalibo bakin zaren tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar baki daya."

Mika mulki cikin lumana shi ne babban burin al'ummar kasar Kongo, kuma hakan shi ne zai tabbatar da zaman lafiya, kwanciyar hankali da ci gaban kasar ta Kongo, har ma da nahiyar Afrika baki daya, in ji mista Ma. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China