Cikin wata sanarwa, mambobin kwamitin sun ce tuni aka riga aka gabatar da korafe-korafe, gaban kotun tsarin mulkin kasar, suna kuma karfafa gwiwar daukacin masu ruwa da tsaki, da su kare yanayin zaman lafiya da aka samu yayin babban zaben da ya gabata, su kuma bi hanyoyin warware sabani da kundin tsarin mulkin kasar, da ma tanaje-tanajen dokokin zaben kasar suka shimfida.
Kwamitin ya ce, yana fatan dukkanin sassan kasar za su kauracewa ta da hankali, su martaba zaman lafiya da lumana da aka samu yayin babban zaben, da ma sakamakon da aka cimma. Kaza lika su mutunta dimokaradiyya, tare da zaman lafiya da lumanar kasar.
Har ila yau, mambobin kwamitin sun yi kira da a tabbatar da hadin kan kasa, da ginin ta bisa tsarin zaman lafiya, da tattaunawar siyasa tsakanin dukkanin masu ruwa da tsaki. (Saminu Hassan)