in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fara taron dandalin tattaunawar tattalin arzikin duniya a Jordan
2019-04-07 16:15:55 cri

Jiya Asabar 6 ga wata bisa agogon kasar Jordan, aka bude taron koli na yankin Gabas ta Tsakiya da arewacin nahiyar Afirka na dandanlin tattaunawar tattalin arzikin duniya karo na 17, inda mutane fiye da dubu 1 a fagen siyasa da kasuwanci daga kasashe fiye da 50 suka fara tattaunawa kan yadda za a kafa sabon dandalin yin hadin gwiwa.

Klaus Martin Schwab, wanda ya kafa taron dandalin tattaunawar tattalin arzikin duniya kuma shugaban zartaswa ya bayyana cikin jawabinsa cewa, yake-yake da tashe-tashen hankula sun dade suna kawo cikas kan bunkasuwar tattalin arzikin yankin Gabas ta Tsakiya da arewacin nahiyar Afirka. Makasudin taron dandalin tattaunawar tattalin arzikin duniyar shi ne domin kafa wani tsarin yin tattaunawa na dindindin, a kokarin kara azama kan warware wasu batutuwa masu sarkakiya na yankuna, kamar halin da ake ciki a kasar Iraki, da batun kasar Syria, da rikici tsakanin Palasdinu da Isra'ila, da kuma batun 'yan gudun hijira. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China