in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta koka game da karancin kudin taimakawa wadanda guguwar Idai ta shafa a yankin Kudancin Afrika
2019-04-06 15:36:05 cri
MDD ta ce ba a amsa sosai ba, game da kiran da ta yi na neman kudin gudanar da ayyukan agaji ga miliyoyin mutanen da mahaukaciyar guguwar Idai ta sha a yankin kudancin Afrika.

Stephane Dujarric, Kakakin Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya bayyana cewa, a kasar Mozambique da guguwar ta fi shafa, kaso 21 na dala biliyan 282 da ake nema kadai aka samu.

Ya bayyana haka ne bisa dogaro da bayanan da ofishin kula da harkokin agajin jin kai na majalisar da abokan hulda a fanni ayyukan agaji da kuma kasashen da guguwar ta aukawa, suka bayar.

Adadin wadanda suka mutu da gwamnatin kasar Mozambique ta bayar a baya bayan nan, ya kai 598, inda ake tsammanin karuwarsa saboda samun hanyar shiga sauran yankuna da iftila'in ya shafa.

A Zimbabwe kuwa, abokan hulda na ayyukan agaji da gwamnatin kasar, sun kaddamar da asusun neman tallafi ga kasar, inda suke neman dala biliyan 60 domin agazawa mutane 270,000 da mahaukaiyar guguwar ta shafa.

Gwamnatin Zimbabwe ta tabbatar da mutuwar mutane 299 yayin da wasu 300 suka bata.

Ayyukan agaji a Malawi kuwa na bukatar dala miliyan 26, domin cika dala miliyan 45.2 da ake bukata na gudanar da ayyukan agaji. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China