Tijjani Muhammad-Bande, ya yi wannan kiran ne a Litinin din nan, albarkacin ranar MDD ta kasa da kasa, ta tunawa da al'ummun da cinikin bayi da kuma safarar bil Adama ta tekun atlantika ya shafa.
A cewar sa, yayin da ake cika shekaru 400 da kawo karshen cinikin bayi ta tekun atlantika, ita ma majalissar shugabannin kasashe mambobin kungiyar hadin kan Afirka ta AU, a zaman ta na watan Fabarairun da ya gabata, ta yi suka game da yadda aka aikata laifuka na muzgunawa, da ayyukan rashin imani, yayin cinikayyar bayi ta tekun atlantika. Kaza lika ta yi tir da yadda aka kafa wani tsarin nuna wariyar launin fata, da kuntatawa, da nuna kyama da tursasawa bil Adama.