Mataimakin Sakataren kungiyar, Collins Mgbo ne ya nuna bacin ran kungiyar, cikin wata wasikar da kungiyar ta aikewa hukumomin kasar a ranar Laraba.
Mgbo ya ce, an jiwa 'yan Nijeriya bakwai rauni, a lokacin hare-haren da ake ci gaba da kaiwa, uku daga cikin su ma a yanzun haka suna kwance ne a Asibiti, domin raunukan na su sun yi tsanani, inda suke barazana ga rayuwarsu.
Ya ce, akwai bukatar sa bakin gwamnatocin kasashen na Afrika ta kudu, da Nijeriya cikin gaggawa, musamman kan yanda rikicin ke kara tabarbarewa.
Har dai zuwa lokacin hada wannan rahoton, ba labarin mutuwar wani dan Nijeriya, duk da cewa an bayar da labarin mutuwar 'yan kasar waje biyu a sakamakon harin," in ji wasikar ta Mgbo.