in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
ECA: Akwai bukatar Afirka ta samar da tsarin tattalin arziki mai nagarta da zai hade dukkanin sassa
2019-03-22 10:04:31 cri
Darakta mai kula da sashen tattalin arziki da jagoranci a hukumar MDD mai lura da bunkasa harkokin tattalin arzikin nahiyar Afirka Adam Elhiraika, ya ja hankalin kasashen dake nahiyar, da su dage wajen samar da wani managarcin tsari mai karko, wanda zai hade dukkanin sassa, muddin dai nahiyar na fatan cimma nasarar bunkasa, da kaiwa ga muradun ci gaba na kasa da kasa.

Adam Elhiraika, ya yi wannan kira ne cikin wata sanarwa, yana mai cewa cimma muradun ci gaba mai dorewa, da muradun Afirka na ci gaba nan da shekaru 50 masu zuwa wato zuwa shekarar 2063, ba za su kai ga nasara ba, har sai an samar da tsare tsare na inganta da hade sassan tattalin arziki.

Jami'in na hukumar ECA ya kara da cewa, nahiyar Afirka na matukar bukatar manufofi na fadada da sauya tsarin masana'antun ta, da kuma inganta sha'anin hada hadar kasuwanci tsakanin kasashen nahiyar, musamman karkashin tsarin yarjejeniyar gudanar da cinikayya cikin 'yanci ta AfCFTA.

Elhiraika, ya kuma jaddada bukatar rage tasirin hadurra da tattalin arzikin duniya ke haifarwa ga kasashen nahiyar, kamar tarnaki ga kasuwannin kasa da kasa, da yawan sauyawar farashin kudaden musaya, da zirarewar kudade, da hauhawar farashin hajoji.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China