in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afirka CDC ta yaba da tallafin kasar Sin a fannin inganta kiwon lafiya
2019-04-05 16:16:17 cri

Shugaban sashen tsare tsare da harkokin diflomasiyyar kiwon lafiya, a cibiyar kandagarki, da dakile yaduwar cututtuka ta Afirka ko Afirka CDC a takaice Benjamin Djoudalbaye, ya jaddada muhimmancin tallafin da kasar Sin ke samarwa a fannin kiwon lafiyar al'ummar nahiyar Afirka.

Benjamin Djoudalbaye ya bayyana hakan ne, yayin zantawar sa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a ranar Alhamis, yana mai cewa Sin na cikin kasashe na kan gaba da suka yi hadin gwiwa da cibiyar Afirka CDC, biyowa bayan bayyana bukatar hakan, bayan da shugabannin kasashe mambobin kungiyar AU suka amince da kafa cibiyar.

An kafa Afirka CDC ne a hukumance a shekarar 2017, tana kuma aiwatar da wasu ayyuka da aka tsara cikin shekaru 5, wato tsakanin shekarar 2017 zuwa 2021, wadanda suka maida hankali ga sanya ido, da tattara bayanai kan yaduwar cututtuka, da kuma daura damarar tunkarar matsalolin lafiya na gaggawa da shawo kan su.

Jami'in ya ce Sin na tallafawa ayyukan Afirka CDC a dukkanin sassan 5. Kaza lika tana samar da tallafin kwarewa, da na kayayyakin aiki da ake bukata a cibiyar. Baya ga wannan, Sin na tura kwararru dake ba da shawarari game da ayyukan cibiyar ta Afirka CDC.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China