in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Tunisia: kila ba zai shiga zaben shugaban kasar a bana ba
2019-04-07 16:13:59 cri

Jiya Asaba 6 ga wata, shugaba Beji Caid Essibsi na kasar Tunisia ya ce, ba shi da aniyar shiga babban zaben shugaban kasar mai zuwa, amma ya zuwa yanzu bai tsai da kudurinsa na karshe kan batun ba tukuna.

Shugaba Essibsi, ya bayyana hakan ne yayin da yake halartar wani taron jam'iyyar Nidaa Tounes a wannan rana, inda ya kara da cewa, kamata ya yi 'yan kasar su zabi sabon shugabansu, wanda zai jagoranci kasar ta Tunisia wajen fita daga mawuyacin hali. Tunisia na bukatar sauye-sauye. Akwai matasa kwararru masu dimbin yawa a Tunisia. Kamata ya yi a kara ba su damarmaki. Amma duk da haka shugaban kasar ya nuna cewa, yanzu lokaci bai yi ba da zai tsaida kudurinsa. Zai bayyana ra'ayinsa ne a lokacin da ya dace.

Za a gudanar da babban zaben shugaban kasar Tunisia a ranar 17 ga watan Nuwamban bana. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China