Duk a jiya Talata, Beji Essebsi, shugaban kasar Tunisia, ya gana da shugaba Obiang a fadar shugabancinsa, inda suka ganewa idanunsu yadda aka kulla yarjeniyoyi da dama tsakanin bangarorin 2 masu alaka da ayyukan lafiya, da yawon shakatawa, da aikin noma, da dai sauransu. A cewar shugaba Obiang na kasar Guinea Bissau, ziyarar da ya kai Tunisia a wannan karo na tare da dimbin nasarori da ma'anar tarihi, saboda haka kasarsa na sa ran ganin kara yin hadin gwiwa tare da Tunisia. Ya kara da cewa, za a baiwa 'yan kasar Tunisia damar shiga Guinea Bissau cikin 'yanci ba tare da bukatar neman samun izinin shiga ba, kana za a kafa ofishin jakadancin kasar Guinea Bissau a hedkwatar kasar Tunisia.
A nashi bangaren, shugaban kasar Tunisia, Beji Essebsi, ya nuna maraba da matakan da kasar Guinea Bissau za ta dauka, ya ce Tunisia na son raba fasahohin da ta samu a fannonin siyasa da yawon shakatawa ga kasar Guinea Bissau, sa'an nan za a yi kokarin neman kara kyautata huldar dake tsakanin kasashen 2.(Bello Wang)