in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalisar dokokin Tunisia ba ta amince da gwamnatin kasa ba
2016-07-31 13:08:12 cri
Jiya Asabar, majalisar dokokin kasar Tunisiya ta ki amincewa da gwamnatin kasar, lamarin da ya sa gwamnatin ta kasance ta wucin gadi.

A wannan rana, majalisar dokokin kasar Tunisiya ta jefa kuri'a kan shirin amincewar gwamnatin kasar da firaministan kasar Habib Essid ya gatabar mata, inda wakilai 191 suka halarci taron, haka kuma, wakilai 118 daga cikinsu suka jefa kuri'ar kin amincewa da wannan shiri, yayin da 3 suka jefa kuri'ar nuna amincewa, sa'an nan, akwai wakilai 70 da ba su jefa kuri'ar ba, kaza lika, akwai wakilai 27 da ba su halarci wannan taron ba.

Bisa tsarin mulkin kasar Tunisiya, shugaban kasar zai nada wakilin da zai kafa gwamnatin kasar cikin kwanaki goma masu zuwa, sa'an nan, wakilin zai gabatar da sabbin jerin mambobin gwamnati ga majalisar dokokin kasar cikin wata guda, daga bisani kuma, majalisar dokokin kasar za ta sake jefa kuri'ar nuna amincewa kan gwamnatin ko a'a.

Kafin kafa sabuwar gwamnatin kasar Tunisiya, gwamnatin Essid za ta kasance gwamnatin wucin gadi ta kasar. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China