in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Harkokin yawon shakatawa sun farfado a Tunisia
2017-08-27 13:45:26 cri
Sakamakon matakan yaki da ta'addanci da Gwamnatin kasar Tunisia ta dauka, an samu kyautatuwar yanayin tsaro a kasar, al'amarin da ya haifar da karuwar adadin masu zuwa yawon shakatawa a bana tare da farfadowar bangaren yawon shakatawa na kasar.

Tun daga farkon bana, kasashen Belgium da Sweden da Finland da Denmark da Norway da Iceland da Birtaniya suka soke kashedin da suka sanya wa jama'arsu, tare da amince musu zuwa kasar Tunisia don yawon shakatawa.

Bisa kididdigar da aka yi, a farkon watanni 7 na bana, yawan mutanen da suka shiga kasar Tunisia daga kasashen waje ya zarce miliyan 3 da dubu 500, wanda ya karu da kashi 30 cikin dari bisa makamancin lokacin a bara.

Ana sa ran yawan mutane masu yawon shakatawa na kasashen Turai da kasar Tunisia za ta karba a shekarar 2017 zai kai kimanin miliyan 2, wanda zai karu da kashi 30 cikin dari bisa na bara. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China