Yayin taron da ya gudana jiya Alhamis, kasashen biyu sun rattaba hannu kan yarjeniyoyi 9 a bangarorin da suka shafi tattalin arziki da tsare-tsare da fasahohi da kuma cinikayya.
Har ila yau, kasashen sun rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna ta fuskar kare hakkin masu sayan kayayyaki da kuma tabbatar da ingancin kayayyaki da ayyuka.
Firayiministan Algeria Abdelmalak Sellal, ya ce hadin gwiwa tsakanin kasashen Algeria da Tunisia a bangarori da dama, alama ce dake nuna karfin dangantakar dake tsakaninsu, yana mai alakanta nasarar da kyakkyawar huldar dake tsakanin shugabannin kasashen wato Abdelaziz Boutaflika na Aljeria da takwaransa na Tunisia Beji Caid Essebsi. (Fa'iza Mustapha)