in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan ci rani 58 sun rasu sakamakon nutsewar jirginsu a gabar tekun Tunisia
2018-06-05 09:53:14 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar Tunisia Khalifa Chibani, ya ce yawan 'yan ci rani da suka rasu, sakamakon nutsewar jirginsu a ranar Lahadi a gabar tekun kasar dake kudu maso gabashi ya kai mutum 58.

Khalifa Chibani ya ce cikin wadanda suka rasa rayukansu akwai 'yan kasar 31, da 'yan kasashen waje 22, sauran kuma ba a kai ga gane daga ina suke ba.

Ya zuwa yanzu dai tawagar sojojin ruwa, da na kasa, da jami'an ba da agajin jin kai na kasar, sun ceto 'yan ci rani dake yunkurin ketara tekun kasar ta barauniyar hanya su 68, ciki hadda 'yan Tunisia 60, da kuma wasu baki su 8.

Jami'in ya kara da cewa, da yammacin ranar Asabar, dakarun tsaron kasar ta Tunisia suka cafke wasu mutane 8, wadanda ake zargi da shirya safarar bil Adama ta tsibirin Kerkennah. Tsibirin dai na cikin wurare mafiya shahara, da masu safarar mutane ke amfani da su, wajen fitar da bakin haure zuwa kasashen Turai daga Tunisia.

A cewar hukumar kasa da kasa mai lura da bakin haure, daga farkon wannan shekara zuwa yanzu, kimanin 'yan kasar 1,910 ne suka tsallaka zuwa kasar Italy ta teku. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China