in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban CRI ya ba da kyauta ga makarantar Confucious ta kasar Tunisia
2016-09-25 12:44:56 cri
Shugaban gidan rediyon CRI mista Wang Gengnian wanda ke ziyarar aiki a kasar Tunisia, ya gana da shugaban makarantar Confucious karkashin gidan rediyon Sifax na kasar mista Rashid Hamruni, a ranar Jumma'a da ta gabata, inda ya ba da kyautar wasu littattafai da fina-finan bidiyo na koyon Sinanci.

A yayin ganawar, shugaban CRI ya ce duk da cewa akwai nisa tsakanin Sin da Tunisia, amma jama'ar kasashen 2 suna samun karin fahimtar juna tsakaninsu. Hakan ya tabbata, a cewar shugaban, dalilin ayyukan kafofin watsa labaru, da kuma taimakon da makarantar Confucious ta samar. Don haka, shugaban ya nuna godiya ga mista Rashid kan kokarinsa na taimakawa jama'ar bangarorin 2 ta fuskar musayar ra'ayoyinsu, musamman ma a fannin al'adu, da kuma yadda yake tallafawa aikin gidan rediyon CRI.

A nasa bangare, mista Rashid ya ce jama'ar kasar Tunisia na da bukatar koyon Sinanci sosai, don haka akwai makoma mai haske ga aikin koyar da Sinanci, da yada al' adun kasar Sin a kasar Tunisia. Yana cike da fatan ganin za a rika raya makarantar don kara dankon zumuncin tsakanin kasashen 2. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China