in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yi ya yi bayani kan batun bashi a nahiyar Afirka
2019-01-04 11:04:26 cri
A jiya Alhamis, mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar, Wang Yi ya gana da takwaransa na kasar Habasha Workneh Gebeyehu, a Addis Ababa, sa'an nan jami'an biyu sun gana da manema labaru.

A wajen taron, wani dan jarida ya tambayi Wang Yi ra'ayinsa game da matsalar bashi da wasu kasashen Afirka ke fuskanta cewa wai " sakamakon hadin gwiwa da kasar Sin". Dangane da batun, jam'in kasar Sin ya amsa cewa, wasu mutane suna ta kokarin kururuta "matsalar bashi a Afirka", kuma suna neman dora wa kasar Sin alhaki, lamarin da ya sabawa gaskiya, wanda kasashen Afirka ba za su yarda ba.

Jami'in ya kara da cewa, matsala a fannin yawan cin bashi wani batu ne na tarihi, ba wani abun da ya bullo da shi yanzu ba, kuma ba wani abun da kasar Sin ta haddasa ba. Sa'an nan, kasar Sin tana baiwa kasashen Afirka bashi ne, bisa niyyar da jama'ar kasashen suka dauka, da nufin biyan bukatun kasashen. Sam ba ta taba gindaya wani sharadin siyasa ba. Ban da haka, tana gudanar da aikin bisa doka, ba ta taba hakuri da cin hanci da rashawa ba.

A karshe, jami'in ya ce, matakin da za a iya dauka don daidaita matsalar bashi shi ne, raya tattalin arzikin kasashen Afirka don ya samun ci gaba sosai. Don haka kasar Sin za ta kara kokari wajen aiwatar da sakamakon taron dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka da ya gudana a birnin Beijing a shekarar 2018, da taimakawa kasashen Afirka cimma burinsu na raya tattalin arzikinsu. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China