in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
WHO: An fara allurar riga kafin Ebola a jamhuriyar dimokaradiyyar Congo
2018-05-22 09:21:21 cri
Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta ce an fara gudanar da allurar riga kafin cutar Ebola mai saurin hallaka bil Adama a jamhuriyar dimokaradiyyar Congo DRC, a wani mataki na gaggauta dakile yaduwar cutar da ta sake bulla a wasu sassan kasar.

An fara gabatar da allurar riga kafin ne ga jami'an lafiya dake aiki a yankunan da cutar ta yi kamari, inda ake sa ran a yiwa sauran al'ummun yankunan ita.

WHO ta ce an samar da wadannan allurai da yawansu ya kai sama da 7,500 ga yankunan lardin Equator dake arewa maso yammacin kasar, inda ake hasashen mai yiwuwa ne mutane 46 sun kamu da cutar, yayin da ya zuwa ranar Juma'a aka tabbatar da rasuwar mutum 26 daga cikin adadin.

Daraktan hukumar WHO Dr. Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ce riga kafin daya ne daga muhimman matakan dakile yaduwar wannan annoba, ya kuma jinjinawa abokan huldar hukumar, bisa tallafi da suka bayar wajen tabbatar da nasarar fara riga kafin. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China