Mataimakin Darakta Janar na sashen kiwon lafiya na kasar Anban Pillay da ya bayyana hakan, ya ce baitulmalin kasar za ta samar da kudaden tabbatar da samar da ingantaccen kiwon lafiya iri daya, a bangarorin Gwmanati da masu zaman kansu.
Da yake jawabi a wajen taron kwamitin masu samar da kudaden kiwon lafiya a Rustenburg, Pillay ya ce za kuma su gyara matsalar rashin duba marasa lafiya a kan lokaci.
Ya kara da cewa, za a samar da wurin bada magani ga masu cututtuka masu tsanani domin rage cunkoso a asibitoci.
A cewar Benjamin Musenbi Nganda, jami'in hukumar lafiya ta duniya WHO, akwai bukatar tabbatar da yankunan karkara da birane na samun kiwon lafiya iri daya. (Fa'iza Mustapha)